A yunkurin da ake na hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, Hukumar NDLEA tayi muhimmin kamu inda ta cafke wata mata da tayi fasakaurin hodar iblis har dauri dari kuma tayi dabarar boyesu cikin al'aurarta. Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta cafke wata mata 'yar Najeriya mai zama a kasar Brazil mai suna Mrs Anita Ugochinyere Ogbonna da hodar iblis dauri dari Wanda ta yi dubarar boyewa a cikin al'aurarta da kuma jakar hannu, an cafke ta ne a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe International Airport (NAIA) Abuja, Kamar yanda jaridar daily trust ta ruwaito. Mai Magana da yawun Hukumar , Femi Babafemi, ya bayyana haka a Abuja ranar Lahadi a Abuja, yace matar mai 'ya'ya uku an kama ta ne ranar Jumu'a da dare jim kadan bayan saukar tana Abuja ta hanyar jirgin Qatar Air da ya taso daga Sai Paulo, ta kasar Brazil wanda suka yada zango a Doha, Qatar kafin isowarsu gida Najeriya. Yace bayan binciken ƙwaƙwaf sunyi nasarar ga...