An daure matashin da ya kashe uwarsa ya ciyarda karensa namanta
Abin ban haushi da ban mamaki baya karewa a duniyarnan .
An yankewa want matashi dan kasar spaniya hukuncin daurin shekara goma sha biyar a gidan yari bayan ya kashe mahaifiyarsa tare da yin gunduwa -gunduwa da gawarta.
An kama Alberto Sánchez Gómez mai shekara 28 ne a shekarar 2019 bayan da ƴan sanda suka gano sassan jiki a gidan mahaifiyar tasa - wasu ma an zuba su a robobi.
Kotu ta yi watsi da hujjojinsa na cewa yana fama da taɓin hankali ne a lokacin da ya yi kisan.
A yanzu zai shafe shekara 15 a gidan yari kan laifin kisan kai sannan zai yi wata biyar kuma kan laifin wulaƙanta gawa.
An kuma yi masa umarni ya biya ɗan uwansa diyyar dala 73,000, kwatankwacin naira miliyan 36.
Ƴan sanda sun isa gidan ne a gabashin birnin Madrid a watan Fabrairun 2019, bayan da wata abokiyar arziki ta nuna damuwa kan irin rayuwar da María Soledad Gómez da ke cikin shekaru 60 ke ciki.
A yayin shari'ar, kotun ta saurari ƙara kan yadda Sánchez, mai shekara 26 a wancan lokacin, ya maƙure mahaifiyarsa yayin da suke wata sa-in-sa.
Daga nan sai ya yi gunduwa-gunduwa da sassan jikinta cikin mako biyu, yana ciyar da karensa daga naman.
Kafofin yaɗa labaran Spaniya sun ce dama ƴan sanda sun san halinsa na yadda yake cin zarafinta sannan kuma ya bujirewa umarnin da aka ba shi a lokacin kama shi.
Comments
Post a Comment