Posts

Showing posts from July, 2021

Wata sabuwa: wasu da ke yiwa Elrufa'i kamfen a facebook sunce zasu daina

Image
 A cewar matasan dai sun ce Elrufa'i baya tausayin mutanen Kaduna kuma akan haka sun yanke shawarar goge shafin Facebook da suke amfani dashi wurin yi masa kamfen din takarar shugaban kasa 2023 . Sun ce zasu dauki matakin nan da kwanaki goma sha huɗu masu zuwa. Wasu masu cibiyar shafin suma ba'a bar su a bayaba wajen tofa albarkacin bakinsu kamar yadda zaku gani a hotunan dake kasa.

Hukumar NDLEA ta cafke wata mata da hodar iblis data boye a al'aurarta.

Image
 A yunkurin da ake na hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, Hukumar NDLEA tayi muhimmin kamu inda ta cafke wata mata da tayi fasakaurin hodar iblis har dauri dari kuma tayi dabarar boyesu cikin al'aurarta. Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta cafke wata mata 'yar Najeriya mai zama a kasar Brazil mai suna Mrs Anita Ugochinyere Ogbonna da hodar iblis dauri dari Wanda ta yi dubarar boyewa a cikin al'aurarta da kuma jakar hannu, an cafke ta ne a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikwe International Airport (NAIA) Abuja, Kamar yanda jaridar daily trust ta ruwaito. Mai Magana da yawun Hukumar , Femi Babafemi, ya bayyana haka a Abuja ranar Lahadi a Abuja, yace matar mai 'ya'ya uku an kama ta ne ranar Jumu'a da dare jim kadan bayan saukar tana Abuja ta hanyar jirgin Qatar Air da ya taso daga Sai Paulo, ta kasar Brazil wanda suka yada zango a Doha, Qatar kafin isowarsu gida Najeriya. Yace bayan binciken ƙwaƙwaf sunyi nasarar ga...

Apc ba zata samu gwamna ba - Sen. Kabiru marafa

Image
Kamar yanda bayanai suke fitowa, sun nuna cewar jigo a jam'iyyar apc , sanata Kabiru marafa ya kalubalanci sauya shekar gwamna Bello matawalle zuwa apc saboda ayyana shi da akayi a matsayin jagoran APC a jahar inda yace sam ba zata sabuba   A cewar sa itafa kotun koli ta yanke hukunci cewa jam'iyyar Apc rasa kujerar Gwamna da 'yan majalisu a Zamfara Don haka yace shifa a iya saninsa wannan sauya shekar da gwamna yayi da 'yan majalisu daga PDP zuwa Apc to sabawa wancan hukunci ne da kotu tayi a baya Rashin jituwa sai faman ruruwa yake a cikin jam'iyyar Apc a Zamfara bayan sauya shekar gwamna Matawalle daga PDP zuwa jam'iyyar. Jigon jam'iyyar a jahar ya tsaya kai da fata cewa lallai wannan sauya shekar sabawa hukumcin kotun ƙoli ne, wanda ya ayyana cewa jam'iyyar Apc batada ɗan takarar gwamna a zaɓen 2019 a jahar. Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ARISE News, yayi gargadi cewar jam'iyyar zata fuskanci babban kalubale muddin ba...